Mazauna Katsina-Ala sun tona asirin masu kashe jama’a a Benuwai

0

Wasu ‘yan kungiyar Shi’a da ke zaune a cikin Karamar Hukumar Katsina Ala cikin jihar Benuwai, su na zargin wasu ‘yan bangar da gwamnatin jihar ta daure wa gindi su na kashe mutane kuma su na sace wasu ko kuma su yi garkuwa da su.

Mazauna yankin sun rubuta takardar kuka ga Fadar Shugaban Kasa, da kuma kungiyoyin kare jama’a na cikin gida da na kasashen duniya.

Sun bayyana sunan kungiyar wadannan ‘yan banga da Civilian Joint Task Force, CJTF, wadanda suka ce gwamnati ce ke daukar nauyin su.

A cikin wata takardar kuka da suka rubuta tun a ranar 27 Ga Yuli, 2017, wadda mutane 20 su ka sa wa hannu a madadin sauran mazauna yankin, sun ce irin ta’addacin da CJTF ke aiwatarwa kan mazauna yankin ya yi matukar muni kwarai.

Sun ce ana cin zarafin mata da kananan yara, a bugi wasu, a daure wasu, a karkashe ko kuma a sace a yi garkuwa da wasu.

Sun ce wani mai suna Aondona Ishenge ne da aka fi sani da Tor-Abaji ne babban gogarman ‘yan bangar.

Sun ce za a iya bankado asalin wannan bala’i da su ke fuskanta tun da CJTF su ka kashe wasu mutane biyu, Orkar Galbbom da Wangyo Mnatsav a cikin kauyen Utyondu da ke cikin gundumar Mbayongo. Kisan inji su, an yi shi ne cikin watan Nuwamba, 2016.

Sun kuma ce an kara yin kisan a cikin Janairu, 2017, a Tse-Igbe da kuma cikin watan Yuli, 2017 a Tor-Abaji, inda wasu ke shigar sojoji dauke da zabga-zabgan bindigogi su ka rika kashe mutane su na kuma kona gidajen su.

Sun kara da cewa wasu da ke da sauran kwana a gaba da suka kubuta bayan an yi awon gaba da su, su ne suka rika bada labarin wadanda su ke yin wannan kisan-gilla da satar jama’a.

Sun kuma bada labarin irin yadda su ke samun goyon baya ga gwamnatin jihar Benuwai.

Bayan wannan, masu wannan korafin sun bayyana cewa sun sha kai kara da koken su ga jama’an tsaro, amma ba su yi komai ba.

Bayan PREMIUM TIMES ta samu wannan kwafin takardu, ta nemi jin ta bakin gwamnatin jihar Benuwai, amma abin bai yiwu ba har zuwa lokacin da mu ka buga wannan labarin.

Ga takardar koken nan, dauke da sunayen wadanda aka karkashe da ranaku da kuma garuruwan da aka kashe su.

Share.

game da Author