Sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Suleiman Hunkuyi ya fito kakara don nuna rashin jin dadin sa ga yadda gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ke mulki a jihar Kaduna.
” Yanzu fa munja daga, ko ana ha maza ha mata dole mu wancakalar da El-rufai daga wannan kujera a Kaduna.
Sule ya yi wannan bayanai ne a wajen taron kaddamar da sabuwar kungiyar sa mai suna ” APC Aspirant Forum”.
Ya ce zai iya takarar kujerar gwamnan jihar, kuma ya kafa wannan kungiya ne domin a karya alkadarin wannan karfi na kujeran mai mulki da akan ce.
” A shirye muke sannan zamu kafa ‘ya’yan jam’iyya na gari kuma ‘yan siyasa domin tabbatar da wannan abin da muka sa a gaban ya tabbata.
” Za a tsaftace jam’iyyar APC tun daga kasa har sama sannan za mu tabbatar wadanda za su fafata a jam’iyyar yan jam’iyyar ne na asali kuma masu kishin jam’iyya.
Ya ce dole ne duk ya’yan jam’iyyar su zo su hada hannu da wannan kungiya domin ceto jihar Kaduna daga matsalar da ta shiga na mulkin kama karya.
Shima Tijjani Ramalan, a nashi tsokacin ya ce babu shakka kungiyar sa na ‘Restoration’ ba za su amince da takarar El-Rufai a zaben 2019. Saboda haka ya tattara komatsen sa ya kara gaba kawai bayan 2019.