Jirgin sama mallakar kamfanin sufurin jirage na DANA Airline, ya saki hanya a jiya Talata, ya nausa cikin jeji a filin saukar jirage na Fatakwal da ke jihar Ribas.
Jirgin daga Abuja ya ke, ya je sauka ne a jiya Talata, amma sai ya zarce iyakar da ya kamata ya tsaya, ya rufta cikin jeji.
An tabbatar da cewa ba a rasa rayuka ba, kuma matuka jirgin da sauran fasingoji sun fita daga cikin jirgin lafiya.
Kamfanin DANA ya dora laifin afkuwar haka a kan rashin kyawon yanayi, su na mai cewa, “matukin jirgin ya gamu da rashin kyan yanayi da kuma guguwa mai karfi yayin da ya ke sauka daga sama.
Kamfanin DANA ya jinjina wa matukan jirgin ganin yadda su ka yi namijin kokarin sarrafa jirgin har su ka samu suka tsayar da shi.
Ita ma hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jirage ta ce rashin kyan yanayi ne ya haddasa waskewar da jirgin ya yi cikin jeji.
Har ila yau DANA ya ce zai ci gaba da kula da rayuwa da dukiyoyin fasinja fiye da yanzu, domin dama fasinja ne su ke yi wa aiki.