HARIN BOKO HARAM: An kasa gano inda ’yan mata da yawa su ke

0

Wata daliba mai suna Aishatu Abdullahi, ta na daya daga cikin dalibai matan da suka kubuta daga farmakin Boko Haram a garin Dapchi da ke cikin jihar Yobe, ta ce ba dukkan dalibai matan makarantar ne su ka kubuta ba.

Kamar yadda ta yi bayani, ta ce akwai fa yiwuwar wasu matan na hannun ‘yan Boko Haram an gudu da su.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ba a ta ita hakkake cewa ko da gaske akwai wadanda aka arce da su din ba.

Shi kuwa kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, Sunmonu Abdulmaliki, ya shaida wa PREMIUM TIMES a jiya Talata da dare cewa, tabbas an kai wa makarantar hari, amma babu takamaimen cewa an gudu da wasu dalibai mata daga makarantar.

Ya ci gaba da cewa a yanzu dai kama daga makarantar zuwa iyayen yara, ana ta bi domin a tantance wadanda ke nan makaranta da suka dawo bayan harin da kuma wadanda su ka gudu gidan iyayen su.

“Saboda akwai dalibai kusan 900 a makarantar, kuma wasu daga cikin su sun shiga cikin gonaki, wasu kuma ba su koma makarantar ba. Amma dai na tabbatar da cewa ya zuwa gobe zan samu cikakken bayanin halin da ake ciki daga ma’aikatar ilmi, domin a ji ko an gudu da wasu ko kuma ba a gudu da su ba.”

GARIN DAPCHI

Boko Haram sun kai wa garin Dapchi hari ranar Litinin da dare, abin da ya ja mutanen garin ciki kuwa har da daliban Makarantar Sakandare ta Mata, GGSS Dapchi su ma su ka gudu cikin jeji.

Kai da jin muryar yarinyar da ta zanta da wakilin PREMIUM TIMES, ka san a gigice ta ke, ta fita daga hayyacin ta sosai. Ta zanta da shi ne ta wayar tarho, inda ta ce “maharan sun je ne da nufin kwasar su a matsayin ganima, amma sai yawancin mu mu ka runtuma cikin jeji bayan mun tsallaka katanga da shingen wayar makarantar.”

Dalibar ta yi magana ne a lokacin da ta ke kan hanyar ficewa daga Dapchi, bayan hutun mako daya da aka yi sanarwar an bai wa daliban. Ta ce, “da ido na na ga Boko Haram sun tasa keyar wasu daliban mata sun yi gaba da su.”

Idan har ta tabbata cewa an gudu da wasu daliban mata, harin kenan ya yi kama da wanda aka kai cikin watan Afrilu, 2014, inda aka gudu da sama da daliban Chibok 200 daga sakandaren garin Chibok, jihar Barno.

Yanzu dai kusan shekaru hudu kenan tun bayan sace wadancan daliban da aka yi.

Aishatu wadda ta yi wa wakilin mu magana da Hausa, ta ce jami’an tsaro ba su tarbi maharani ba, har sai da Shugaban Makarantar ta nemi a kai dauki daga gidan da su ke a boye, wanda ba shi da nisa da makarantar.

Share.

game da Author