Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana yadda gwamnati ke kokarin ganin ta magance rikicin makiyaya da manoma da ake fama da shi cikin jihohi da dama a kasar nan.
A cikin bayanin, Osinbajo ya amsa wata tambaya ce wadda ke da dangantaka da batun tsaro a kasar nan.
An yi masa tambaya ne a kan yanzu wane kokari gwamnati ke yi a kan matsalar tsaro?
Osinbajo ya amsa da cewa matakan da gwamnati ta dauka su ne ta tura ‘yan sandan kwantar da tarzoma a wuraren da ake fama da tashe-tashen hankula, har ma da sojojin kasa da na sama. Misali, ka ga an tura sojoji a Jihar Benuwai a yankin garuruwan Guma, Logo, Katsina-Ala da Agatu.
Cikin kwanakin nan kuma sojoji sun tura dakaru a kananan hukumomin Awe da Tunga na cikin jihar Nassarawa. Sannan kuma wasu sojojin na can a Takum jihar Taraba.
Discussion about this post