Shugaba Jacob Zuma ya sauka daga kujerar mulkin Kasar Afrika ta Tudu

0

A daren Laraba ne shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya sauka daga kujerar mulkin Kasar.

Idan ba a manta ba an dade ana kai ruwa rana tsakanin shugaba Zuma da Jam’iyyar sa ta ACN.

Wannan karon fadar ta fi karfin sa don jam’iyyar ta bashi dama ya sauka daga kujerar mulki da kan sa ne ko kuma ‘ya’yan jam’iyyar su tsige shi a majalisa ranar Alhamis.

Zuma ya shekara takwas ya na mulkin Afrika ta kudu.

Mataimakin sa kuma shugaban jam’iyyar ACN ne zai dare kujerar mulkin kasar.

Share.

game da Author