Yadda maciji ya hadiye miliyan 36 a dakina – Philomena

0

Philomina Chieshe ta bayyana wa hukuma shirya jarabawar shiga jami’o’in kasar nan cewa wani shirgegen maciji ne ya lunkume kudin katin jarabawa da dalibai suka siya a jihar Benuwai.

Philomena ta fallasa kanta ne a gaban wata kwamiti da hukumar ta kafa don bincikan inda kudaden suka shiga, babu su kuma babu labarin su.

” Bari in gaya muku gaskiya, nima abin ya bani tsoro domin mai aiki na ne ta fallasa komai a coci. Ta fadi cewa idan tazo wajen da nake ajiyan kudin sai taga wani shirgegen maciji ya doso wajen, inda a bisani sai ya hadiye wannan kudi loma-loma. ”

Abin dai ya ba masu sauraren ta dariya, inda aka kora ta gefe domin sauraren sauran ma’aikatan da suka lashe miliyoyin hukumar.

Idan ba a mata ba sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani daga jin haka ya garzaya mazabar sa da ke Kadunainda ya dauko masu kama maciji, ya ko kai su hukumar don kamo wannan maciji, a kwato wa al’umma kudin su.

Share.

game da Author