Jagoran ‘Yan adawan Zimbabwe Morgan Tsvangirai ya rasu

0

Jagoran ‘Yan adawar tsohuwar gwamnatin Robert Mugabe na kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai ya rasu.

Sanarwar rasuwar sa ta fito ne da ga jam’iyyar sa na MDC, in da suka ce ya rasu ne a dalilin cutar daji, mai suna ‘Colon Cancer’ da yayi fama dashi.

Sanarwar ta kara da cewa Tsvangirai ya rasu a daren Laraba yana da shekaru 65 a wani asibiti dake kasar Afrika ta Kudu.

Idan ba a manta ba Morgan Tsvangirai ya wahala sosai a wajen tsohuwar gwamnatin Kasar, inda sau da yawa ya sha zaman kurkuka da tsangwama daga gwamnatin Mugabe.

Share.

game da Author