Gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 2.2 domin gyara hanyar zuwa filin jiragen sama mai suna ‘Bill Clinton Airport Drive.
Ministan Abuja Muhammad Bello ya bayyana cewa titin na matukar neman gyara ganin cewa tun a 1980 ne aka gina ta.
Gwamnatin ta ce za ta ware wasu kudaden da suka kai Naira miliyan 273 don siyo kayan aikin da za a bukata don samar da tsaftataccen ruwa a Abuja.