Gwamnatin Filato ta kirkiro sabbin ma’aikatu 6

0

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya kirkiro sabbin ma’aikatu shida Kari da 17 jihar me Jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Rufus Bature ne ya sanar da haka sannan ya ce a lissafe dai yawan ma’aikatun gwamnati yanzu sun kai 23.

Bature yace gwamna Simon ya yi haka ne domin gwamnati ta iya sauke nauyin biyan bukatun mutane da ya rataya a kanta:

Ma’aikatun da aka kirkiro sune:

1. Ma’aikatar sufuri

2. Ma’aikatar ma’adinai

3. Ma’aikatar tsara birane

4. Ma’aikatar tattalin arziki

5. Ma’aikatar aiyuka na musamman da aiyuka tsakanin ma’aikatun gwamnati.

6. Ma’aikatar kimiya

Bature ya ce kwamishinonin da aka nada za su fara aiki ne da zarar majalisar jihar ta kammala tantance sunayen da aka mika gabanta.

Share.

game da Author