An dakatar da haya da baburan Keke Napep a manyan titunan Jos

0

Gwamnatin jihar Filato ta kafa dokar hana ‘yan keke NAPEP bin titunan garin Jos da Bukuru.

Jami’in gwamnati Shiolbial Cornelius ya sanar da haka wa manema labarai a yau Litini inda ya kara da cewa dokar ya ba jami’an tsaro damar kama duk wani matukin keke da ya bi wadannan tituna.

Masu tuka keke Napep a garin Jos sun gudanar da zanga-zangar nuna fushin su ga yadda gwamnati ke tatsan su kullum da sunan haraji.

A lokacin da suke wannan zanga-zanga sun barnata wasu gine-ginen gwamnati dake kan manyan titunan Jihar.

Share.

game da Author