Yau ne wani shugaban matasa na kasuwar Maganin dake karamar hukumar Kajuru jihar Kaduna mai suna Yahaya da aka fi sani da ‘Dan Najeriya’ ya bayyana wa PREMIUM Times ta wayar hannu cewa rikici ya barke a kasuwar inda sanadiyyar haka an bankawa shaguna da gidaje da dama wuta.
Yahaya yace an fara samun tashin hankula ne bayan wasu matasa sun ki yarda wasu ‘yan mata mazauna yankin su canza addinin da suke Kai zuwa wani addinin da bam.
” Ina mai tabbatar muku cewa wasu matasa sun bankawa shaguna da dama wuta a wannan kasuwar sannan mutane da dama sun sami raunuka kuma ni da idona na ga gawar mutum uku.”
Jim kadan bayan haka, gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya aika da Karin jami’an taro yankin sannan ya umurce su da su tabbata sun taso keyar duk wanda ya ke da hannun a wannan tabargaza.
Bayan haka kuma ya umurci hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar da ta kai kayan agaji yankin domin Tallafawa wadanda suka rasa dukiyoyin su a hargitsin.
Discussion about this post