NDE: Za a horas da ‘yan gudun hijira sana’o’in hannu

0

Hukumar samar da akin yi ta kasa (NDE) reshen jihar Adamawa ta fara horas da ‘yan gudun hijira da wadanda suka fara komawa garuruwansu a jihar da suka kai 2,500 sana’o’in hannu.

Jami’in hukumar Kenneth Maigida wanda ya sanar da haka a sansanin Malkoh dake kusa da garin Yola ya ce bayan hukumar ta gudanar da bincike kan sana’o’in da zai fi dacewa da ‘yan gudun hijirar da jihar baki daya ne suka fara wannan shiri.

Ya ce hukumar za ta horas da ‘yan gudun hijiran sana’o’in hannun da suka hada da kiwon kaji, kwaliya,girki da sauransu.

Mai gida ya kara da cewa a yanzu haka hukumar NDE na horas da matasa marasa aikin yi sana’o’in hannu da suka kai 2000 a jihar inda wasu cikin su za a yayesu a watan Afirilu

Share.

game da Author