HARIN JAMI’AR MAIDUGURI: Hankali ya kwanta

0

A daren Litini ne daliban jami’ar Maiduguri dake jihar Barno suka yi kwanan tsaya sanadiyyar tashin bam a kusa da katangar jami’ar.

Bisa ga bayyanan da wasu daliban suka sanar wa PREMIUM TIMES sun shaida mana cewa sanadiyyar harbe wani dan kunan bakin wake ne da sojojin da ke gadin jami’ar suka yi ya sa bam din dake rataye a jikin sa ya tashi.

” Sojojin dake gadin jami’ar mu sun fada mana cewa sun harbe wani dan kunar bakin wake ne da suka ga yana kokarin kutsa kai cikin jami’ar.

Daliban sun ce a yanzu haka suna ci gaba da gudanar da harkokin su duk da cewa suna zaman dardar a makarantan.

Share.

game da Author