MAI RABON GANIN BADI: Yadda jirgin fasinjojin Abuja zuwa Jamus ya kusa tunkuyar kasa

0

Fasinjojin jirgin kamfanin sufuri na Lufthansa, sun ga bala’i kuru-kuru, a lokacin da jirgin da su ka hau daga Abuja zuwa birnin Frankfurt na Jamus, ya sadaro kasa, daga nisan kafa dubu 35,000 sai da ya zo daidai kafa dubu 5,000 tsakanin sa da kasa.

PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa fasinjojin sun tsallake rijiya da baya ne a rananr Lahadi, bayan da jirgin mallakar kamfanin kasar Jamus, ya sadaro kasa, da misalign 11:15 na dare.

Cikin kowane fasinja ya duri ruwa, jim kadan bayan da jirgin ya tashi daga filin jirgin Abuja, amma ba zato ba tsammani, sai ya sadaro kasa, kai ka ce zai fado ne, yadda gaba daya kowa ya firgita a cikin jirgin.

Fasinjan ya shaida cewa lokacin da al’amarin ya faru, awa daya da rabi daidai bayan jirgin ya cira sama, yayin da jirgin ya suntumo kasa, sai da wasu fasinjojin da ba su daure da bel din su suka fadi kasa, wasu ma sun ji raunuka, sannan kuma wasu da yawa kayan su ya rikito daga inda suka ajiye su.

Fasinjan nan ya ci gaba da cewa saboda tsananinn tsoro, ba a raba musu abinci ba, kuma ma’aikatan da ke karakaina a cikin jirgin kowa ya yi bakam kamar ruwa ya ci shi.

Ya ce su kuma mahukuntan jirgin sun ce matsalar ta faru ne sakamakon rashin kyan yanayi da kuma matsalar wani inji na jirgin, amma ba wani mutum ne da gangan ya haddasa matsalar ba.

A lokacin da su ka isa Jamus, sun ga motocin daukar marasa lafiya ko gawarwaki da kuma motocin kashe gobara sun yi sahu su na jiran fasinjojin da za a sauke, wadanda su kuma tun ma kafin a sauka kowa ya rigaya ya yi “sallama da duniya.”

Kokarin da PREMIUM TIMES ta yi na yin magana da mahukuntar kamfanin jirage na Lufthansa bai yi nasara ba a yau Talata.
An kira su amma ba su dauki waya ba. An kuma yi sakon tes, amma har yanzu ba su maida amsa ba.

Share.

game da Author