WAWURAR DUKIYA: Kotu ta kori shari’ar Tsohon Gwamna Nnamani

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, ta kori karar da EFCC ta kai tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, a bisa dalilin rashin gamsassun cajin da ake tuhumar sa.

Lauya mai kare Nnamani, Rickey Tarfa, ya shaida wa kotu cewa ai wanda ya ke karewar ya shigar da koken cewa mai shari’a Mohammed Yunusa ya rufe sauraron shari’ar tun kara mai lamba ta FHC/L/09c/07.

Ya ce tunda har wanda ya ke karewa ya shigar da amincewa zai sasanta a gaban kotun Yunusa, don haka Mai shari’a Obiozor ba shi da hurumin da zai saurari karar da aka daukaka a kan Nnamani.

Sai dai lauyan EFCC, Kelvin Uzozie, ya nemi a sake kakkabe fayil din case din domin zai sake gabatar da wasu sabbin tuhuma kan Nnamani.

Mai shari’a ya ce tunda dai akwai batun sasantawa da wanda ake kara ya amince a yi da shi ya bayar da abin da ya sani ke hannun sa, wato plea bargain, don haka ya soke karar, ya kore ta.

Share.

game da Author