NAZARI: Kafin fetur ya babbake gwamnatin APC

0

Man fetur, walau danyen sa ko tataccen sa, ya na a sahun gaba na kayan albarkatun kasa da ya fi martama da daraja a duniya. Babu lokacin fadin martabar sa ko auna gejin darajar sa a wannan rubutun. Amma dai a Nijeriya ma fetur, danyen sa ko tataccen sa, shi ne tushen duk wani alheri da kuma sharri a kasar nan.

Duk wata gwamnati, ta tarayya, jiha da kakanan hukumomi, da fetur su ke takama, idan an sayar a raba riba duk wata a ba su, a yi aiki da wani kaso, wani kason kuma a sace. Biyan albashin ma’akata, kudin fetur ne. biyan ‘yan kwangila kudaden ayyuka, kudin fetur ne. Komai dai fetur, fetur, fetur.

ALHERI DA SHARRIN MAN FETUR

Idan mu ka haska madubin sharri kuwa, za mu ga duk wata babbar sata a kasar nan, kudin fetur ne aka sace. Duk wani babban barawo, ko dan Kudu ko dan Arewa, to barawon kudin fetur ne, ko da kuwa a wata hukuma mai kula da harkokin addini ce aka sace kudin.

Ba za ka san fetur na da daraja ba, sai a lokacin da ya ke wahala. Za ka ga fetur ne kawai matasala a lokacin, amma matsalar sa ta shafi kowane bangare na rayuwa a kasar nan. Idan farashin sa ya tashi, sai farashin komai ya tashi, hatta tsinken ashana shi ma sai ya yi fikafiki ya tashi sama.

Duk da irin darajar da fetur ke da shi, a daya bangare kuma, fetur ne babban bala’i a kasar nan. Duk da irin kaunar sa da zame mana tilas da ya yi a rayuwa, fetur shi ne abin da aka fi yin kaffa-kaffa da shi. Gobarar sa ta fi gobarar-daji bala’i. Kadan kyes fetur ke jira, yanzu sai ya babbake dukiya ta bilyoyin nairori.

Ba Gwamanatin Muahammadu Buahri ce farau wajen fuskantar matsalar fetur ba.

Hasali ma, Buhari ya gaji wannan matsala ce daga hannun gwamnatin Goodluck Jonathan. Shi din ma, dukkan shugabannin da aka yi a kasar nan kafin shi, sun sha fama da matsalar.

Inda matsalar fetur da ake fama da ita ta gwamnatin Buhari ta fi sauran ta gwamnatocin baya tayar da hankali da kuma zama alakakai da jangwam ga al’ummar kasar nan, wuri biyu ne, ko kuma a ce uku.

Na farko, tun da ake gwamnati a Nijeriya, ta Buhari ce aka zaba musamman don ta yi maganin matsalolin da kasar nan ke fama, musamman ta man fetur da sauran manyan matsaloli.

A cikin watan Janairu, 2012, Buhari na sahun gaba wajen botsare wa gwamnatin Jonathan wajen kin yarda a kara farashin man fetur, da kuma batun cire tallafin man fetur. A lokacin da ya ke kamfen, shi da jam’iyyar sa APC, sun yi alkawarin maida lita daya ta fetur naira 45, daga naira 87 a lokacin.

AN YABA SALLAR APC, TA KASA ALWALA:

Sai dai kuma ba a dade da rantsar da Buhari ba, sai wata guguwar matsalar fetur ta tirnike gwamnati da kasa baki daya. Gwamantin APC ta rasa yadda za ta yi, inda ta yi ta dawurwura a wuri daya, daga karshe ta ce ta cire tallafin man fetur, sannan kuma an maida lita daya daga naira 87 ta koma 145.

Gwamantin ta yi haka ne don man ya rika wadata da kuma wasu dalilai da talakawa ba su gamsu da su ba. Sai dai kuma inda Buhari ke samun nasara kan ‘yan Nijeriya, shi ba a yi masa zanga-zanga kamar wadda aka yi wa Jonathan ta zaman-dirshan a cikin Janairu, 2012 ba.

Mummunan karancin mai da aka yi kwanan nan, da ya yi sanadiyyar yin bukukuwan Kirsimeti da na Sabuwar Shekara a cikin halin kunci, ya gigita kasar nan sosai. Ba a gama fita daga cikin kangin ba, sai Karamin Ministan Harkokin Fetur, Ibey Kachukwu ya cukurkuda hankalin ‘yan Nijeriya ya ce musu tabbas farashin da ma ake saida litar fetur daya a kan naira 145 ba zai dore ba, domin gwamnati idan ta sayo fetur, ya na iso mata ne har saukewa akan naira 171.

Duk da dai ya ce gwamnati ba za ta kara farashi ba, amma duk mai hankali, da maras hankalin, sun san nan gaba kadan tilas a kara farashin litar man fetur. Musamman tunda Kachikwu ya furta cewa a duk wata Nijeriya na asarar naira bilyan 900 idan ana saida lita daya a kan naira 145.

TSAKA-MAI-WUYAR GWAMANTIN BUHARI

Tsaka-mai-wuyar da gwamnatin APC ke ciki shi ne, a baya ta shimfida wa talakawa alkawurran ciyar da su da shayar da su romon dimukradiyyar da ba su taba sha ba da kuma wanda ta ce aka tauye musu ba su sha ba, tun daga ranar da aka bai wa Nijeriya ‘yanci, har zuwa 20145.

A maimakon haka, tun daga hawan gwamnatin Buhari, babu wani farashin kaya da ke sauka, sai dai tashi. Man fetur ya tashi, kananzir ya tashi, gas ma ya tashi. Haka farashin shinkafa, doya, gero, wake,masara, auduga, da dukkan kayan masarufin da takala ke tutiya da shi a rayuwar sa ta hannu-baka-hannu-kwarya, da su kan su kayan alatu.

Kwanaki da wa’adin gwamnatin APC ne kawai ke raguwa a tsawon shekaru ukun da ta shafe ta na mulki, amma komai ya tshi, ko an tsawwala shi.

Babban farashin da ya tashi kuma ya yi wa tattalin arzikin Nijeriya dabaibayin-jakin-kuturu, shi ne farashin Dalar Amurka, wanda ya ke tsakanin naira 190 zuwa 220 kafin Buhari ya hau mulki. A yanzu kuwa ta kai naira 360 a kasuwar-shinko.

Takaicin da talakawa ke yi shi ne, duk wadannan abubuwa da suka kara farashi, su ne Buhari da APC suka rika kururuwar cewa za su saukaka wa al’umma idan sun hau mulki. Amma maimakon a samu sauki, sai kara hauhawa su ka yi.

Tun ana bai wa gwamnatin APC uzuri, har ta kai a yanzu an fara yi mata kallon ita da PDP din duk Danjuma ne da Danjummai.

HANNU DAYA BAYA DAUKAR JINKA:

Har yanzu a Arewacin kasar nan akwai dimbin mutanen da bas u yarda gwamnatin Buhari na tafka kura-kurai ba, haka kuma bas u ma so su ji masu adawa na ambaton kura-kuran.

A yayin da su ke ta hakilon kare hwamnatin, tuni sauran yankunan kasar nan sun yi nisa wajen fara kware wa gwamnatin baya. Yawanci a Arewa sun kasa fahimtar cewa kuri’un shiyya ko yanki daya, ba su zama abin dogaro ga dan takarar shugaban kasa.

KIBIYAR AJALI…

Ganin yadda aka ci kwakwar wahala a shekarun nan uku, akwai jan aiki a nan gaba. Za a sha kallon yadda gwamnatin APC za ta yi wasa da kura ba tare da takunkumi a wurin kamfen ta na cewa a zake zaben ta domin komai ya saukaka a 2019.

Matsalar man fetur din nan zai iya gurgunta APC, musamman ganin cewa saura shekara daya da wata daya a sake zabe, ga shi kuma karin farashin fatur za zame wa ‘yan Nijeriya tamkar ajali, wanda ko ba-dade, ko ba-jima sai Buhari ya kara kudin kafin zabe mai zuwa.

Za a zuba ido a gani, ko talakawa za su yarda a kara wa fetur farashi? Shin karin kudin fetur nan gaba zai zama kugiyar lankwara tattalin arzikin kasar nan ya koma bisa turba, ko kuwa zai zama kibiyar ajalin gwamnatin APC?
Kaka-tsara-kaka!

Share.

game da Author