Gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi malaman jihar da kada su kuskura su amsa Kiran Kungiya Malamai reshen jihar Kaduna NUT na fara yajin aiki daga gobe litinin.
A wata takarda da kakakin Gwamnan jihar ya sa wa hannu, ya bayyana cewa gwamnatin ba za tayi kasa-kasa ba wajen hukunta dak wani malami da ya biye wa kungiyar malaman.
Gwamnati ta ce babu wanda ya ke da iko akan ma’aikatan ta musamman ganin cewa abinda take yi kan malaman jihar, tana yi ne don ta gyara harkar ilimi a jihar sannan ta taimaki ya’yan talakawa da suke karatu a irin wannan makarantu.
Ta ce ta umarci ko wani makaranta a jihar ta dauki sunayen malamai da suka zo aiki da wadanda basu zo ba daga gobe litinin.
Su ko kungiyar malamai na jihar, sun wasa wukar su, sun ce babu gudu ba ja da baya.
Sakataren kungiyar NUT Adamu Ango ya ce sun ba gwamnati wa’adin makonni biyu su dakatar da maganar korar malamai a jihar amma sunyi musu kunnen uwar shegu. A dalilin haka yasa zasu fara yajin aiki sai yadda ta yiwu.
” Bayan haka wasu ababen da muke kuka da su sun hada da yi wa malaman sakandare ritaya gangarangan, ba tare da sun kai lokacin yi ba.
Sannan kin biyan malamai 3,338 kudaden hutun su na shekarar 2015, da kin biyan malaman jihar kaf kudaden hutun su na shekarar 2016 da 2017.
Sannan har wa yau akwai malamai 15,000 da ba a biya su bashin albashin su ba tun shekarar 2015.