Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Kawankwaso, ya soke ziyarar da yayi niyyar yin gangamin kaiwa jihar Kano gobe Linitin.
A wata sanarwa da ya yi wa manema labarai a Gidan Kwankwasiyya da ke Luggard Avenue, Kano, Rabi’u Bichi ya bayyana cewa an soke ziyarar ne domin a samu zaman lafiya sannan kuma a kauce wa kashe-kashe, ganin cewa gwamnatin Abdullahi Ganduje ta shirya yaki da tawagar Kwankwaso.
Rabi’u Bichi, wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Jihar Kano a lokacin mulkin Kwankwaso, ya nuna cewa saboda son zaman lafiyar Sanatan na su, tun da ya damka wa Ganduje mulki a cikin 2015, bai je Kano ba, sai fa ta’aziyyar mahaifiyar Ganduje da ya je yi kawai.
Ya ce Kwankwaso ya yi haka ne domin ya kyale Ganduje ya tafiyar da mulkin sa kawai.
Ya ce sn yi tunanin janye ziyarar ce saboda shawarwarin da abokan arziki da sauran jama’a suka bayar cewa a hukara kawai daga yin wannan ziyara, gudun abin da ka iya biyo baya.
Da ya ke kara nuni da cewa Kwankwaso mutum ne da ba zai so abin da zai tashi hankula ko ya haifar da rasa rayuka ba, ya kara da cewa nan gaba za su shaida wa magoya bayan su abinda ake ciki.