Jami’in hukumar yaki da yaduwar cutar kanjamau na jihar Gombe Suraj Abdulkarim ya ce babu abin da suka iya tabukawa game da hana yaduwar cutar kanjamau a jihar saboda rashin kudi.
Ya ce sun shiga wannan matsala ne sakamakon janye tallafin da suke samu daga kungiyoyin bada tallafi da babban bakin duniya.
“Kudaden da muke samu daga kungiyoyin da babban bakin duniya ta kai miliyan 100 sannan tun da suke janye kudaden da muke da shi baya isar mu aiwatar da aiyukkan mu.”
Abdulkarin ya ce duk da haka sun sami ragowar yaduwar cutar daga kashi 3.4 bisa 100 zuwa 3.2 bisa 100 a 2017.
Daga karshe ya yi albishir cewa da zarab sun sami kudaden da suke bukata za su inganta aiyukkansu ne a yankunan karkara ta hanyar tabbatar da cewa duk mata masu ciki sun yi gwajin cutar kanjamau domin sanin matsayin su da kare ‘ya’yan dake cikinsu.