An falla wa wata Sanata mari

0

Rincimi ya tashi a safiyar yau Litinin a Majalisar Tarayya, bayan da wani ma’aikacin majalisar ya falla wa Sanata Abiodun Olujimi mari.

Olujimin ita ce Mataimakiyar Bulalar Majalisar Dattawa. Al’amarin ya faru ne a lokacin da su ke kokarin halartar taron sauraron kwamitin harkokin man fetur na majalisar dattawan.

Rikicin ya kaure ne a lokacin da wani ma’aikacin majalisar ya hau na’urar kai mutane sama, tare da ita sanatar, wato ‘lift’, wadda aka ware wa Sanatoci da Mambobin Majalisar Tarayya.

Dama a wurin an ware wadda sai ‘yan majalisa ne kadai za su shiga, a gefe daya kuma akwai ta sauran game-garin jama’a.

PREMIUM TIMES ta gano cewa sanatar da mai marin kowa na ta kokarin tafiya halartar taron da ke gaban sa ne. Shi ma’aikacin ya na hanzarin halartar taron kungiyar su ne ta ma’aikatan majalisar tarayya, da ke shirin tafiya yajin aiki.

Wanda aka yi marin a kan idon sa ya bayyana cewa a lokacin da sanatar ta ga wannan ma’aikacin a cikin ‘lift’ daya tare da ita, sai ta nemi ta san ko shi wane ne da har zai shigo cikin na’urar daukar jama’a daya tare da ita.

Ganau ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa nan take sai sanatar ta sa daya daga cikin hadiman ta ya mari wannan ma’aikaci.

Shi kuma wanda aka mara, bai tsaya wata-wata ba, sai kawai ya yanke sanatar da mari, maimakon ya rama a kan wanda ya mare shi.

Bayan sun fita daga ‘lift’, sanatar ta tunkari wanda ya mare ta, amma sai abokan aikin sa suka tare masa fada, maimakon ma su ba ta hakuri.

An ce sun hau ta da hargowa da hayagaga, da kyar jami’an tsaro su ka fice da ita daga zoben da suka yi mata, kamar za su cinye ta danya.

Ta bayyana wa manema labarai cewa za ta kai magana a gaba, tunda dai an san wanda ya yi marin.

Share.

game da Author