Gwamnatin Yobe zata biya dalibai likitoci albashi duk wata

0

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da cewa za ta fara biyan dalibai likitoci 110 albashi duk wata.

Maitaimaka wa gwamnan jihar kan yada labarai Abdullahi Bego ne ya fadi haka ranar Alhamis inda ya ce wadannan dalibai likitoci kari ne kan wasu 389 da tun can suna samun albashi a jihar.

Bego yace a lissafe gwamnati za ta kashe Naira miliyan 41, 392, 560 wajen biyan dalibai duk shekara.

Daga karshe ya ce bude kwalejin likitoci da asibitin koyarwa na jami’ar Yobe ta yi zai taimaka wa fannin kiwon lafiya a jihar.

Share.

game da Author