Atone- Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Taraba Yusufu Akirikwen ya shaida wa gwamantin tarayya cewa basu da filayen da za su iya badawa domin kirkiro Burtololi wa makiyaya a jihar wato ‘Colonies’.
Ya fadi haka ne a garin Jalingo da yake ganawa da manema labarai.
Ya ce gaskiyar magana itace mafi yawan ‘yan Najeriya basu san me ake kira Burtali ba wato ‘Colonies’.
” Sannan ta yaya gwamnatin tarayya za ta samo wadannan filayen da take magana akai? Shin zama za ta yi a Abuja ta yanko filayen daga jihohin kasar ko yaya?’’
Akirikwen yace a yanzu haka jihar tana kokarin kafa doka da zai samar wa makiyaya a jihar rigogi don kiwata dabobin su a killace sannan suna sa ran cewa dokar za ta fara aiki daga ranar 24 ga watan Janairu.
” Dokar za ta ba makiyaya ‘yancin siyan filaye domin kafa rigogin su na kiwata dabobin su a killace.”
Discussion about this post