2019: Zaben PDP ce mafita ga matsalolin Najeriya, Inji Atiku

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ba za su yi nadama ba muddun suka sake zaben jami’yyar PDP a kasar nan.

Shugaban gidauniyyar ‘Atiku Care Faundation’ Aliyu Ibn Abbas wanda ya wakilci Atiku a walimar yi masa maraba da dawowa jami’yyar PDP daga APC da Zainab Pindar ta shirya a Arewa House dake Kaduna ranar Lahadi.

Atiku ya kara da cewa jam’iyyar PDP ce kadai jam’iyyar da zata iya gyara Najeriya sannan ta dawo mata da darajar ta da bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ya kuma yi kira ga sauran masoyan jam’iyyar da su sanar da wannan sako ga mutane musamman mazauna karkara.

Atiku ya yabawa Zainab Pindar saboda irin kaunar da ta nuna masa sannan ya yi kira ga sauran matasan kasar nan da su yi koyi da irin abin da ta ke yi.

Daga karshe malama Pindar ta ce za ta yi iya kokarinta don ganin jam’iyyar PDP da Atiku sun sami nasara a Zabe mai zuwa.

Share.

game da Author