Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnatin jihar Katsina da yin almubazzaranci da naira bilyan 400 da jihar ta samu a cikin watanni 31.
Shugaban Jama’iyyar ne, Salisu Majigiri ya bayyana haka a ranar Talata, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Katsina.
Majigiri, wanda shi ne tsohon dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mashi Da Dutsi, ya ce wadannan kudaden duk manyan jami’an gwamnatin Masari ne su ka balle-bushashar su da su.
Ya ce duk da irin wadannan makudan kudade da aka rika damfara wa jihar Katsina a cikin watanni 31, jihar ba za ta yi tutiya da amfana da komai ba, sai tulin bashi da kuncin fatara da talauci a zukatan jama’a.
Shugaban na PDP ya ce a cikin watanni 30 jihar Katsina ta karbi kason naira bilyan 243 daga Asusun Gwamnatin Tarayya, sai kuma wata naira bilyan 30 daga cikin kudaden da ake maidowa daga Paris Club.
“Duk da wadannan tulin bilyoyin kudade da jihar Katsina ta samu, wai duk ba su isa ba, sai da gwamnatin jihar ta rika bin bankunan ‘yan kasuwa, inda ta ciwo bashi maras dalili har na naira bilyan 70.
“Makudan kudade sama naira bilyan 14.5 da gwamnatin PDP ta tafi ta bari a asusun jihar Katsina, sun sa jihar a lokacin ta zama a sahun gaban sauran jihohi mafi nauyin aljihu a lokacin.” Inji Majigiri.
“Duk da irin wadannnan kudade, a l’ummar Katsina ba su ga komai a kasa ba, sai ma mayar da su ’yan maula da aka yi alhali ga dimbin dukiyar su can a hannun gwamnati ana almubazzarantar da ita.”
Sai dai kuma kakakin yada labaran Gwamna Masari, Audu Labaran, ya bayyana cewa dukkan wadannan zarge-zarge ba su da tushe balle makama, kawai ki-fadi ne PDP ke yi.
Labaran ya ce gwamnatin Aminu masari, gwamnati ce mai tafiyar da aiki kan ka’ida tare da kashe kudaden jama’a ta hanyoyin da suka dace ba tare da almubazzaranci ba.
Ya de duk wanda ya san yadda gwamnatin Masari ta ke, kuma ya ga yadda Katsina ta ke a yanzu, to ko da ya ji kalaman Majigiri, ba zai rike su da wani muhimmanci ba.
Discussion about this post