Ban ce zan samar da filaye don gina wuraren kiwo wa Fulani a Filato ba – Gwamna Lalong

0

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya musanta rade-radin da ake ta yadawa musamman a shafunan sadarwa na yanar gizo cewa ya samar da wasu filaye don gina wa fulani makiyaya wuaren kiwo a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar.

Kakakin gwamnan Dan Manjang ne ya sanar da haka a madadin gwamna Lalong.

Ya ce wannan labari da ake ta yadawa karya ce kawai, cewa anayi ne don a bata masa suna a jihar.

” Ana haka ne don a abata wa gwamna Lalong suna kawai amma bai fadi haka sannan bari in kara jaddawa mutane cewa jihar Filato bata da filin da zata ba fulani don kiwo ko kuma kirkiro da dwangwali, wato wuraren kiwo a jiha. Kowa ya kwantar da hankalin sa.”

Share.

game da Author