An gano kwarangwal din mutumin da ya fi kowa dadewa a Afrika

0

Masu bincike sun gano mukamukin wani kwarangwal din da suka yi ittifakin cewa shi ne mutumin da ya fi kowa dadewa a duniyar Afrika.

An samu mukamukin ne a kasar Isra’ila, kuma ya na dauke da hakora bakwai, yayin da rikakkun masana kimiyya suka auna, suka tabbatar dacewa shi ne mafi dadewa da ke wajen Afrika.

Masana kimiyyar sun ce binciken su ya nuna musu cewa mutumin kaura ya yi daga Nahiyar Afrika, tun tuni can baya shekarun da ba a taba zato ba.

Sun yi ittifakin cewa, sinadarin da suka auna a jikin kwarangwal din mukamukin mutumin, ya nuna cewa mutumin ya wanzu ne tsakanin shekaru 177,000 ko ma 194, 000 da suka gabata.

Sun kara kafa hujja da cewa dasashi da hakoran mutumin ko kusa ba su yi kamanceceniya da irin na mutanen da tarihi ya taba bayarwa a shekaru dubbai da suka shude ba.

An dai samu wannan mukamukin ne na habar sa ta sama, ta bangaren hagu. Amma abin da aka iya tabbatarwa shi ne dadewar mutumin ta nuna cewa balagagge ne kafin ya mutu. Sai dai kuma an kasa tabbatar da cewa shin mukamukin na namiji ne, ko kuwa mace ce.

An hako shi a kogon Misliya da ke kan Tsaunin Carmel, kimanin kilomita 12 yamma da Haifa.

Share.

game da Author