An sace wasu mata su uku, dukkan su Dangin Shugaban Karamar Hukumar Munya da ke jihar Neja. Ana zaton cewa masu garkuwa da mutane ne suka sace su.
Rahotanni sun ce an sace ‘yan matan ne a cikin gidan shugaban karamar hukumar a garin su, Kuchi, a ranar Asabar.
Wanda aka yi abin a kan idon sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sai da masu garkuwar suka bude wuta, suka rika surfa harbi a sama, ta yadda suka hana a kai daukun ceton matan.
An ce wadanda su ka yi garkuwar sun kira lambar shugaban karamar hukumar, inda suka shaida masa cewa sun sace dangin nasa mata su uku, amma ba su kai ga fada masa adadin kudin da suke nema daga wajen sa ba.
An kuma ce barayin sun arce ta Dajin Kabula ne, suka boye wadanda suka sace a can.
A nata bangaren, rundunar ’yan sandan jihar Neja ta tabbatar da garkuwar da aka yi da matan. Kakakin su Mohammed Abubakar ya ce tuni sun shiga farautar barayin tare da kudirin ceto rayukan matan uku.
Garuruwan Munya, Suleja da Tafa na fama da masu garkuwa, masu fashi da kuma fitinannun masu aikata kananan laifuka.