Gwamnatin jihar Kogi ta sanar cewa wani likita dake aiki a asibitin gwamnati a Lokoja ya kamu da Zazzabin Lassa.
Shugaban asibitin Olatunde Alabi ne ya sanar da haka, sannan ya ce an gano haka ne bayan gwajin cutar da aka yi wa wannan likita.
Yace a yanzu haka likitan wanda ke da shekaru 30 na nan ya na samun kula a asibitin Irrua.
Alabi ya kuma kara da cewa kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO, ma’aikatar kiwon lafiya na jihar da masu ruwa da tsaki a jihar sun fara tsaro hayoyi domin dakile yaduwar cutar a jihar.
Ya yi kira ga mutane da su yi gaggawan kai duk wanda suka ga ya kamu da zazzabi ta kowace iri ce asibiti sannan su su tsaftace muhallin su da kuma adana kayan abinci nesa da beraye.
Discussion about this post