Sanannen abu ne irin tsananin bukatar da dubban matasa ke da ita na shiga manyan makarantu don cigaba da karatunsu bayan kammala karatun sakandare. Wannan bukata ta fi kamari ga jami’o’i wadanda duk shekara su ke fama da adadi mai yawa na masu neman shiga, adadin da nesa ba kusa ba ya zarce abin da za su iya dauka bisa ka’idodi da Hukamar Jami’o’i ta Kasa wato NUC ta dora musu. Lamarin ya na kara tsananta duk shekara sakamakon yawan dalibai masu neman shiga da yake karuwa su kuma jami’o’in ba a fadada su ba ta yadda adadin da za su iya dauke dukkan maneman ba.
Misali, a shekarar da ta gabata kasha talatin bisa dari (30%) ne kawai daga cikin dalibai miliyan daya da dubu dari bakwai (1.7m) da su ka rubuta jarabawar neman shiga jami’o’i wato UTME su ka samu zarafin a dauke su.
Tsananin kwadayin karatu da son sai kowa ya yi aikin gwamnati da kuma gane cewa ba wani ci gaba mai ma’ana da mutum zai iya samu a rayuwarsa idan bai yi karatun ba su ne kanwa uwar gamin hobbasa da farkawar da matasa maza da mata su ka yi don ganin sun zurfafa ilminsu. Wannan hobbasa ta sa shiga jami’a ya zama wani al’amari mai wahalar gaske.
Misali duk dalibin da ya ke nemen shiga jami’a dole ne sai ya tsalleke wasu matakai da su ka hada da samun nasara a jarabawar kammala sakandare (SSCE) da credit biyar da su ka hada da Turanci (English) da Lissafi (Mathematics), samun nasara a jarabawar UTME wacce hukumar JAMB ta ke shiryawa da kuma samun nasara a jarabawar bayan UTME wato Post-UTME da jami’o’i su ke shiryawa. Sai dai abin takaici shi ne duk da wannan wahala babu tabbas cewa dalibi zai samu a dauke shi a makarantar da ya nema ko da ya samu duk nasarar da ake bukata domin akwai yiwuwar a samu adadi mai yawa na wadanda su ka sami irin wannan nasara ko ma wacce ta fi ta kuma jami’o’in ba su da sararin kwashe su duka.
Wannan matsala ta jima ta na ci wa al’umma, musamman gwamnati da iyaye, tuwo a kwarya. A nata bangaren gwamnati ta na ganin ta na yin iya bakin kokarinta wajen fadada jami’o’in da ake da su ta hanyar kara gine-gine don kara karfin abin da su ke iya dauka da kuma samar da sababbi. A zahirin gaskiya kuma a halin yanzu kusan ba wata jiha a Najeriya wacce babu jami’ar gwamnatin tarayya a cikinta. Sannan kusan dukkanin jihohi su na da jami’a mallakin gwamnatin jiha (Kano guda biyu gareta) baya ga dumbin jami’o’i masu zaman kansu da ake ta kafawa musamman a kudancin wannan kasa. Abin tambaya shi ne me yasa duk da wannan fadadawa lamarin kullum ya ke kara kamari? Masana sun yi ittafaki cewa fadadawar da ake samu ko kusa ba ta kai matsayin bukatar da ake da ita ba musamman idan aka kalli irin yadda yawan al’umma ya ke nunnunkawa.
Tuni dai masu hannu da shuni su ka nemawa kansu mafita ta hanyar kai ‘ya’yansu makarantu masu zaman kansu ko dai a nan gida ko kuma a kasashen waje na Turai, Asia kai har ma nan Afurka. Duk da cewa manazarta na ganin cewa tsame ‘ya’yansu da jami’an gwamnati su ke daga jami’o’inmu na gida ya na bayar da gudunmawa ga halin ko-in-kula da ake nunawa ilmi a makarantun gwamnati a wannan kasa, wasu na ganin cewa hakan yana taimakawa wajen rage tsanani akan jami’o’in kuma zai iya samar da dama ga wasu daliban su maye gurabensu. Ko ma dai menene ra’ayin mutum game da wannan, wani abu mai muhimmanci shi ne irin inganci da nagartar karatun da ake yi a kasashen waje. Dole ne a bawa wannan lamari muhimmanci domin daga karshe ko me aka karanto a waje akwai kwakkwaran zaton cewa nan za a dawo a gabatar da shaidar don neman aiki ko wasu bukatu.
A baya-bayan nan akwai rahotanni ma su tayar da hankali da ake samu na bullar wasu makarantu na boge a garin Kwatano (Cotonou) na Jamhuriyar Benin da suke bayar da kwalayen digiri da za ka iya cewa ba su wuce shaidar zur ba ga dalibai musamman daga Nigeria. Akwai abubuwan zargi da tuhuma game da wannan “karatu” na Kwatano, musamman dan takaitaccen lokaci da ake dauka kafin kammalawa. Maimakon shekaru hudu ko biyar ko ma shida na karatu a nan Najeriya a Kwatano dalibi zai iya kammalawa a shakara daya ko biyu.
Har ila yau makarantun su na bayar da dama ga dalibin da ya fara karatu a nan don yin kaura ya koma can ya ci gaba. Wannan ya na bayar da dama ga dalibai da su ka kammala aji daya ko biyu su koma can. Daga cikin rahotanni da ake da su masu dimautarwa akwai daliba da ta kammala shekara daya anan kafin ta koma can sai ga shi shekara daya da rabi bayan komawarta har ta kammala digiri. Akwai dalibi da shi ma da aka kore shi saboda gazawa a daya daga cikin jami’o’in Najeriya, sai ga shi shekara daya da rabi bayan komawar sa irin wadannan jami’o’i na Kwatano har ya kammala karatunsa ya dawo gida da kwalinsa na “digiri”. Misalai irin wadannan su na nan da dama da su ka sa jama’a da dama kokwanto. Anya kuwa! Anya ba lauje cikin nadi? Akwai rahotanni da dama da su ke nuna cewa irin wadannan dalibai su na tarewa ne a guraren sharholiya da shakatawa kuma hakan ba ya hana su sami sakamako mai kyau kwarai da gaske. Shin ya abin ya ke ne?
Ya kamata hukumar NUC ta bincika ta gano hakikanin abin da ya ke faruwa. Menene ingancin wadannan makarantu? Ya ya tsarin karatunsu ya ke? Menene darajar manhajarsu? Wane tsari su ke bi ake kammala karatu da wuri haka? Ya akai daliban da aka san masu rauni ne su ke samun kyakkyawan sakamako cikin dan kankanin lokaci haka? Wanne dabo ko surkelle ake amfani da shi? Shin su na ma amincewa? Ya wajaba gwamanti ta bincika. Idan an tabbatar ba bu wani kaikayi shikenan. Idan an samu coge ko rashin gaskiya dole ne a yi wa al’umma bayani kuma a hana mutanenmu zuwa.
Sannan dole ne a yi watsi da shaidar da aka samo daga wadannan makarantu a lamarin aiki ko takarar siyaya da sauransu. Bai kamata tsananin son digiri ya sa a kyale mutane su dinga bin kowace irin hanya ba. Ba kawai nan ba, akwai makarantu da ake tafiya a wasu kasashe don yi manyan digirori kamar Masters da PhD wadanda su ma akwai zargin cuwa-cuwa a cikinsu. Dole ne NUC ta bincika ta yi wa al’umma bayani.
Babu shakka motoci ‘yan-Kwatano sun taimakawa masu karamin karfi wajen mallakar abin hawa. Amma bai zama dole ne a amince da digiri dan-Kwatano ba domin ilmi daban mota daban.
Dr. Ibrahim Siraj, is from the Department of Mass Communication, Bayero University, Kano. Email: adhamai@yahoo.com, isiraj.mac@buk.edu.ng
Discussion about this post