‘Yan sanda sun kama Salima ta na kokarin siyar da tagwayen ‘ya’yan ta a Katsina

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wata mata mai suna Salima ‘yar shekara 30 da ta nemi ta siyar da tagwayen ‘ya’yan ta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Besen Gwana ne ya fadi haka da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Katsina.

Ya ce Salima wace ke zama a Marabar-Kankara, karamar hukumar Malumfashi ta yi kokarin siyar da tagwayen ‘ya’yan ta mata da basu wuci watanni biyu da haihuwa ba kan Naira 350,000 wa wani mutumi dan karamar hukumar Faskari.

Ya ce da suka kammala cinikin kudin siyan yaran sai mutumi ya ce mata ta jira shi ya je ya kawo mata kudinta.

” ko da mutumin ya tafi bai tsaya ko ina ba sai a ofishin ‘yan sanda inda ya bayyana mana abin da ya faru tsakanin sa da wannan mata.

Salima ta fada wa manema labarai cewa ta so ta siyar da tagwayen ne batare da sanin mijin ta ba.

Share.

game da Author