FYADE: An yanke wa wasu mazaje biyu hukuncin daurin rai da rai a Bauchi

0

Kotu a jihar Bauchi ta yanke wa wasu mazaje hukuncin daurin rai da rai don aikata fyade wa wata mata mai shekaru 40 da kuma kwakule idanuwarta a kauyen Yelwan Dawani dake garin Toro jihar Bauchi.

Alkalin kotun Rabi Umar ta ce ta yanke wa Mohammed Sani wanda aka fi sani da ‘Bambi’ mai shekara 30 da Sabo Rabo wanda aka fi sani da ‘Bullet’ mai shekara 40 don gamsuwa da ta yi da shaidun da aka gabatar a gabanta wanda ya nuna cewa lalle wadannan mazaje sun aikata hakan ranar 1 ga watan Maris 2014.

Masu laifin sun nemi a sassauta musu amma mai shari’a Rabi bata yarda da wannan roko ba.

Share.

game da Author