Canjin shekar da Atiku ya yi daidai ne, cewar IBB

0

Tsohon Shugaban Kasa na mulkin sojoji, Ibrahim Babangida, ya bayyana cewa canjin shekar da Atiku Abubakar ya yi daga APC zuwa PDP, daidai ne.

Babangida Ya yi wannan bayani ne yayin da Okowa tare da shugaban rikon jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi da wasu manyan PDP suka kai masa ziyara a ranar Labara, a gidan sa na Minna, jihar Neja.

Babangida ya ce Atiku dai dan Najeriya ne, kuma kowa na da ikon canja ceka daga wannan jam’iyya zuwa wata wadda ya ke ganin cewa ta fi masa.

Ya kara da cewa irin wannan ba wani abin mamaki ba ne, ballantana kuma PDP ba wata sabuwar jam’iyya ba ce ga Atiku, ya san ta sosai.

Daga nan sai ya juya kan taron ganganin PDP na kasa da za a gudanar kwanan nan, ya na mai cewa ya tabbatar a wannan karo za a yi gangamin da ya zarce sauran gangamin da PDP ta taba gudanarwa a baya.

Yayin da ya ke magana cikin barkwanci tare da ‘yan jarida da sauran shugaban nin PDP, Babangida ya ce ya na da tabbacin za a yi adalci a wurin zaben da za a yi yayin gangamin wanda za a yi a Abuja.

Makarfi ya ce ziyarar ta su irin wadda aka saba yi ce a al’adance, zuwa wurin iyayaen jam’iyya, domin neman shawarwarin su.

Share.

game da Author