Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Bashir Ahmad

0

Wasu dauke da bindiga sun yi garkuwa da wani mai taimakawa sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani, Bashir Ahmad a unguwan Tudun Wada dake Kaduna.

Bashir Ahmad dai malamin makaranta ne sannan kuma yana taimakawa Sanata Shehu Sani kan harkokin da ya shafi matasa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta sanar da kama wani da ake zargi na da hannu a aikata wannan aiki.

Wani da abin ya faru a gaban sa ya ce masu garkuwan sun zo a mota mai budadden baya inda suka hau shi Bashir da duka kafin ska jefa shi cikin motar suka tafi da shi.

Sanata Shehu Sani ya tabbatar da haka inda ya ce lallai Bashir yana tare dashi ne sannan sai inda man shi yakare wajeb ganin an gano wadanda suka aikata haka sannan da ganin an sako shi.

Share.

game da Author