Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da ta’aziyyar sa ta musamman ga masarautar Katagum kan rasuwar sarki Muhammadu Kabir Umar.
Sarki Muhammadu Kabir ya rasu ranar Asabar, a garin Azare, hedikwatar masarautar sa.
A wata sanarwa da ta fito daga ofishin Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya bayyana Sarkin a matsayin babban rashi ba ga masarautar Katagun da Jihar Bauchi kadai ba, har ma da kasa baki daya.
Shugaban Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Sokoto duk sun aika da sakon ta’aziyyar su ga masarautar, gwamnatin jihar Bauchi da iyalan marigayin.
Sarkin ya taba rike mukamin Ministan Ilimi na Lardin Arewa, a zamanin jamhuriya ta farko, a karkashin mulkin Sardauna.
Marigayi Maimartaba Sarki Muhammadu Kabir ya rasu ya na da shekaru 83.