Awoyi bayan shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ya ziyarci sabon shugaban jam’iyyar PDP Uche Secoundus, kotun daukaka kara ta yanke hukunci yau a Abuja cewa Saraki ya koma hukumar kula da da’ar ma’aikata CCT.
A hukuncin da ta yanke yau kotun ta ce akwai wasu tambayoyi da Saraki bai amsa ba wanda sallamar sa da akayi da ya ba a duba da kyau ba.
Ministan shari’a ya shigar da kara cewa hukumar ta yi kuskure wajen sallamar Saraki kan abubuwan da ake tuhumar sa.