An yi wa yara sama da miliyan 2.6 alluran rigakafin cutar bakon dauro a jihar Kano

0

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta yi wa yara sama da miliyan 2.6 alluran rigakafin cutar bakon dauro a wannan shekarar.

Gwamnatin ta ce hakan ya yiwu ne saboda himmar da suka yi wajen wayar da kan mutanen jihar game da mahimmancin yi wa yara allurar rigakafin.

PREMIUM TIMES ta rawaito cewa sakamakon hakan mutanen karamar hukumar Tarauni sun jinjinawa gwamnatin jihar kan samar da alluran ga mutanen jihar da tayi.

Mutanen garuruwan Kano sun godewa gwamnati kan kula da su da samar musu da irin wannan rigakafi ga ‘ya’yan su.

Wasu da suka tofa albarkacin bakin su akai sun ce kira ga mutanen jihar ya yawaita a dan kwanakinnan da su fito da ‘ya’yan su domin yin rigakafi.

” Mun yi murna matuka game da ganin wannan rana domin a makon da ta gabata babu abin da kake ji a radiyo, talabijin, masallatai da coci-coci illa kira ga iyaye da su zo su yi wa yaran su alluran rigakafin cutar bakon dauro.”

” Gwamnati ta yi matukar kokari wajen wayar da mu domin har gida-gida aka biyo mu ana fada mana mahimmancin yin wannan allura ga ‘ya’yan mu’’.

Haka kuma aka yi a karamar hukumar Gwake inda mutane da dama suka fito da ‘ya’yan su domin yin musu wannan alluran rigakafin.

Wata mazauniyar karamar hukumar Aisha Ismail ta ce bayan ta sami bayanin illar da cutar bakon dauro ya ke iya yi wa yara ta gaggauta yi wa danta alluran.

Bayan haka ma’aikacin cibiyar kiwon lafiya na matakin farko dake karamar hukumar Tarauni Nura Muhammed ya ce kafin su fara yi wa yara allura, suna zaton 10,289 za suyi wa sai gashi a rana ta farko sun yi wa yara 10,509 allura.

Shi kuwa jami’in karamar hukumar Birni da kewaye Mohammed Sani ya ce nasarar da suka samu a 2017 ta fi na shekarar 2015.

Ya ce a ranar farko sun yi wa yara allura 11,400 cikin 62,732 da ake zaton yi wa a karamar hukumarsu.

Jami’in kula da yin alluran rigakafi na jihar Sherrif Musa ya ce duk da zage damtsen da suke yi domin ganin an sami nasara wajen yin alluran ma’aikatan su sun dan ci karo da wasu ‘yan matsaloli da ba a rasa ba.

Daga karshe gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya ce gwamnati ta ware Naira miliyan 75 domin yi wa yaran kananan hukumomin jihar alluran rigakafi.

A takaice dai jihar Kano ta yi wa yara sama da miliyan 2.6 alluran rigakafin cutar bakon dauro a maimakon miliyan 2.5.

Share.

game da Author