Akalla mutane hudu tare da wasu sojoji biyu su ka rasa rayukan su sakamakon wani harin kunar-bakin-wake da aka kai a Pulka, cikin karamar hukumar Gwoza, a jihar Barno.
Sojojin sun mutu ne a wani hari daban, yayin da su ka motar da suke ciki ta taka nakiyar da Boko Haram suka dasa a gefen hanya.
Harin na farko dai wasu kananan ‘yan mata biyu su ka kai shi sanye da riga mai sulkin bam a cikin ta.
Kakakin yada labaran rundunar sojoji a Maiduguri, Onyema Nwachukwu ya tabbatar wa PREMIUM TIMES HAUSA wannan hari da aka kai.
Ya ce a ranar Litinin ne da yamma aka kai harin, yayin da wasu suka hangi wasu ‘yan mata biyu na kokarin kutsawa cikin dandazon jama’a.
“Sojojin mu sun yi nasarar harbe daya daga cikin su kafin ta kai ga shiga cikin jama’a ta tashi bam din da ke jikin ta. Harbin da aka yi mata ne ya sa bam din ya tashi a jikin ta, kuma ya kashe ta.
Nwachukwu ya ce yarinya ta biyu ta samu kai wa cikin gungun jama’a, kuma ta tashi bam din da ke jikin ta.’ Inji Kanar Nwachukwu.
Ya kara da cewa fararen hula biyu sun mutu ne tare da yarinya ta biyu wacce ta tada bam din da ke jikin ta. Su kuma sojoji nakiya ce motar da suke ciki ta taka, ba kwanton-bauna ne Boko Haram suka yi mana ba, kamar yada wasu kafofin yada labarai su ka rika yayatawa.