Har yau har kwanan gobe matatun mai Na kasar nan ba su kasa samun wani tagomashi fiye da gwamnatin da ta gabata. Kuma halin da su ke a yau, bai fi na yadda gwamnatin Buhari ta same su ba.
Wannan sharhi Na PREMIUM TIMES HAUSA zai tabbatar da irin yadda matatun su ka kara tabarbarewa a daidai wannan lokaci da matsalar fetur ta dabaibaye kasar nan.
Wannan matsalar fetur ta kawo babban cikas ga bukukuwan Kirsimeti musamman zirga-zirga da tafiye-tafiye zuwa garuruwa.
Manyan dillalan fetur sun dora laifin a kan Hukumar Kula da Harkokin Fetur ta Kasa, dominnita kadai ce ke shigo da tataccen fetur kuma ta ke raba wa manyan dillalan fetur a kan farashin da ta yanka da kan ta.
Sai dai kuma, yayin da matsalar ke kara kamari, tambayar da ake ta yi cike da mamaki ita ce: me ya sa kasar da ta fi kowace kasa arzikin mai a Afrika ba ta iya tace shi a gida, sai ta shigo da tatacce daga kasashen waje?
Me ya sa aka kasa gyara matatun da mu ke da su a Warri, Fatakwal da Kaduna? Ina alkawarin da aka yi cewa da an hau mulki a,2015?
AN KI CIKA ALKAWARI
Jim kadan bayan hawan sa mulki, Shugaba Muhammadu. Buhari ya sake jaddada alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabe cewa ya dauki alkawarin da ya hau zai gyara dukkan su.
Amma cikin Satumba, 2015, gwamnati ta ce an dan gyara matatun inda ta ce su ma samar da kashi 1.96 kacal na yawan man da ake bukata a kullum a kasar nan.
A cikin Satumba 1996 an ce matatun su na samar da tataccen mai na naira bikyan 9..9, amma kuma ana dirka asara mummuna wadda ta kai naira bilyan 12.4.
Cikin Disamba, 2016, NNOC ta ce za a rika tace dukkan mai da kasar nan ke bukata a matatun Kaduna, Warri da Fatakwal a cikin 2017.
Amma kuma kwatsam, cikin Satumba, 2017, watanni tara bayan alkawarin da aka yi na rika samar da tataccen mai, sai Shugaban NNPC, Maikanti Baru ya yi sanarwar rufe dukkan matatun man kasar nan, domin a yi musu garambawul.
Cikin Disamba, 2015, NNPC ta ce ta fitar tataccen mai har MT 787,490, daga gurbataccen mai MT 1,080,183.
Ko ma dai ya abin ya ke, masana harkokin mai sun ce Nijeriya ba za ta taba ganin karshen matsalar karancin ta kawo karshe ba, muddin ba ta rika tace man da za ta sha a cikin gida da kan ta ba.
Shugaban Kungiyar PENGASSAN, Francis Johnson, ya shaida was PREMIUM TIMES cewa su manyan ma’aikatan hukumar na son ganin Nijeriya ta dawo ta na tace mai da kan ta a matatun ta na cikin gida.
A SAYAR DA MATATUN A HUTA
Wasu ‘yan Najeriya na masu ra’ayin a sayar da matatun ga ‘yan kasuwa kawai. Sai dai kuma Karamin Ministan Harkokin Fetur, Ibe Kachikwu, ya bayyana cewa gwamnati ba ta da niyyar sayar da matatun.
Ya ce idan Dangote ya kammala gina katafariyar matatar man sa a Lagos, za rika tace ganga 600,000 a kullum. Idan aka ganganda da na sauran kananan matatu, zai iya wadatar da kasar nan.