Sanin kowa ne cewa da zaran an ganka kana cin goro musamman Wanda ake cewa macen goro sai kaga ko ana maka kallon bakauye ko dai wani gaja.
An fi jingina cin goro ga tsofaffi.
Daga baya ma wasu da yawa na ganin cin goro na da matukar illa ga lafiyar mai ci.
Ita dai goro aba ce da ake yin amfani da ita musamman a al’adun mutanen kasashen Afrika. A Najeriya, ana yi amfani da Shi wajen kulla zumuci da bukukuwa da ya shafi aure da karrama baki.
Wasu likitoci sun yi kokarin wayar da kan mutane gane da amfani da ita macen goro ta ke da shi a jikin mutum musamman yadda mutane suka canfa cewa yana da lahani a jikin mutum.
Likitoci da suka yi bincike kan amfanin goro sun bayyana ce daya daga cikin amfanin da goro yake yi ya hada da gyara huhun mai shan taba sigari.
Sauran amfani da goro ke yi sun hada da;
1. Magance ciwon kai musamman wanda ake kira da ‘Migrain headache’
2. Maganin zawo ko kuma ‘Atonic Diarrhea’ da turanci.
3. Tana tafiyar da gajiya.
4. Goro na rage kiba musamman ga wadanda suke fama da ita.
5. Tana taimaka wa mutanen da suke fama da kasala saboda tana duke sa sinadarin ‘Caffen’.
6. Tana hana yin amai.
7. Tana kawar da jiri.
8. Goro na maganin ciwon dajin ‘ya’yan marainan namiji
9. Yana maganin mura da cutukan da ya shafi makogoro da hanci
10. Yana hana kamuwa da cutuka
11. Yana warkar da ciwon ciki
12. Yana kara kuzari
13. Yana warkar da matsalar kumburin ciki.
14. Yana bude kwakwalwar mutum
15. Yana taimakawa ga masu matsalar gaba da kara kuzari wajen saduwa da iyali.
Duk da wadannan amfanin da goro take da shi likitoci sun yi gargadi cewa yawan cin goro na da illa a jikin mutum. Sun yi kira da aci da Kula.
Discussion about this post