Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya fadi cewa gwamantin sa za ta horas da dalibai masu takardun kammala karatun koyan malunta wato ‘National Certificate of Education NCE’ da suka kai 5000 a jihar.
Masari ya fadi haka ne a taron marabtan wasu ‘yan jam’iyyar PDP da suka canza sheka zuwa APC da aka yi a karamar hukumar Rimi ranar Alhamis.
Ya ce za su yi haka ne a karkashin tsarin ‘S- Power’ domin bunkasa yanayin koyar wa a makarantun firamaren jihar.
‘‘Wannan tsarin za tayi aiki kamar tsarin ‘N-Power’ da ake yi yanzu sannan tsarin zai taimaka wajen samar wa matasa aikin yi da kawar da talauci a jihar’’.
Ya kuma ce bayan an horas da masu NCE din za a tura su aiki a duk makarantun firamaren dake jihar.
Bayan haka Masari ya nuna farin cikin sa ga irin goyan bayan da mutanen jihar ke ba gwamnatin jihar sannan ya yi kira ga wadanda suka canza sheka daga PDP zuwa APC da su yi biyayya ga dokokin jam’iyyar APC.
Daga karshe daya daga cikin wadanda suka canza shekar Bilyaminu Rimi ya bayyana cewa za su yi WA jam’iyya biyayya kamar yadda ta ke a dokar jam’iyyar.
Discussion about this post