Jiragen ruwa sun iso bakin Tekun Legas dankare da man fetur

0

Kamar yadda ma’aikatan albarkatun man fetur na kasa ya sanar cewa ba za a yi wahalar mai ba duk da rade-radin da ke ta yada wa wai man zai yi wahala a dan kwanakinnan, da yammacin talatan yau wasu manyan jiragen ruwa uku dauke da man fetur da taki suka iso bakin tekun Najeriya.

Bayan haka kuma hukumomin ma’aikatar kula da iyakokin ruwa na Najeriya, NPA, sun ce akwai wasu jiragen dauke da man fetur da abinci guda 26 da ake sauraro za su iso kasar nan daga yau zuwa 30 ga watan Disamba da muke ciki.

Share.

game da Author