Mutane 99 suka rasa rayukan su a hadarin jirgin ruwa a Legas, Kebbi da Neja

0

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya bayyana cewa tsakanin watannin Afirilu da Satumba shekaran nan mutane 99 ne suka rasa rayukan su sanadiyyar kifewar jiragen ruwa a jihohin Legas, Kebbi da Neja.

Binciken da NAN ya yi ya nuna cewa tsakanin wadan nan watanni a jihohin Legas da Neja jirgin ruwa biyu sun kife a rafin Neja inda mutane 47 suka rasa rayukan su sannan wasu sun bace da har wa yau ba a gansu ba.

Sannan hakan ta sake afkuwa ranar 14 ga watan Satumba a jihar Kebbi inda mutane 53 suka rasa rayukan su a wannan rafin Neja.

Gidan jaridar ta gano cewa jirgin ruwan da ta kife a jihar Kebbi na hanyar zuwa kasuwar Poll dake karamar hukumar Bagudo dauke da ‘yan kasuwa 100.

” mutanen da suka iya ruwa 500 sun iya tsamo mutane 47 daga cikin 100 da jirgin ruwa ta kife da su rafin Neja.”

Hakan ta sake faruwa ranar 15 ga watan Afirilu a jihar Kebbi inda mutane 7 suka rasa rayukan su yayin da jirgin ke hanyar dawowa daga kasuwan Malali dake karamar hukumar Ngaski.

Share.

game da Author