2019: INEC ta fito da sabbin dabarun hana magudi – Jami’in INEC

1

Wani babban jami’in Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ya bayyana cewa hukumar ta kirkiro wata hanyar fasaha inda za ta rika watsa sakamakon zaben 2019 daga rumfunan jefa kuri’a zuwa hedikwatar hukumar ta kowace jiha.

Kwamishinan Zabe na Ebonyi, Godwill Obioma ne ya bayyana haka yayin da ya ke taro da shugabannin addinai da kungiyoyin addinai a yau Talata, a Abakaliki.

A ta bakin sa, wannan sabuwar fasaha na daga cikin kokarin da hukumar zaben ta yi domin magance magudi, zamba a lokacin zabe da sauran asarkala, domin a tabbatar da sahihanci da inganta ayyuka nagari yayin gudnanar da zabe.

Obiona ya kara tabbatar wa dukkan masu kada kur’a cewa kuri’ar su za ta yi tasiri, kuma ita ce mafita a zaben 2019.
“INEC na kara inganta sabon tsarin da muka shigo da shi wanda za a rika tura sakamakon zabe daga mazabu kai tsaye zuwa hedikwatar hukumar a jihohi.

“To fatan mu shi ne wannan sabuwar fasaha, Allah ya sa ta yi abin da ake son ganin ta yi, domin a yi amfani da ita a zaben 2017.

“Wannan sabon tsari zai kawar da harkallar kwace akwatun zabe, dankara wa akwatin zabe na kuri’un rinto da kuma sauran laifukan da suka dabaibaye harkar zabe.

“Mu a yanzu sakon mu ga jama’a guda daya ne. kowa ya fito ya yi rajista, kuma ya tabbatar ya karbi katin shaidar rajista na PVC domin shi ne zai ba ka dama da ‘yancin zaben wanda ka ke so.”

Taron wanda aka yi da shugabannin kungiyoyin addinai, an gudanar da shi ne domin a hada karfii don a wayar wa jama’a kai su garzaya su fara yin rajistar shirin zaben 2019.

Haka kuma an nemi su zaburar da matasa ‘yan shekaru 18 abin da ya yi sama, su garzaya su yanki rajistar zabe.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa kungiyoyi 50 ne suka halarci taron, ciki har da wakilan Kwamitin Koli na Addinin Musulunci da kuma Kungiyar Kiristoci ta Kasa, CAN.

Share.

game da Author