Wasu daga cikin gwamnoni da masu fadi aji na jam’iyyar PDP sun yi ganawar sirri da gwamman jihar Sokoto, Aminu waziri Tambuwal a garin Asaba.
Tambuwal ya ziayarci garin Asaba, babban birnin jihar Delta ne don halartar bukin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar Okowa ya yi.
A wannan ganawa, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da tsohon gwamnan Delta, James Ibori duk sun halarci bukin.
Wasu masu sharhin siyasa sun ce wannan ganawa dai yana da nasaba da shirin da jam’iyyar PDP keyi domin tun karar zabukan 2019.
Jaridar Daily Trust ne ya ruwaito wannan labari.