TAMBAYA: Menene musulunci ya ce akan saka zoben Azurfa, shin yana da asali?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Sayan zoben Azurfa nada asali a musulunci, fiyayyen halitta Annabin mu Muhammadau Sallallahu Alaihi wa salam, ya sanya zoben azurfa kuma yayi umurni ga wani sahabin sa da idan zai sanya zobe to, ya sa na azurfa.
Maza da mata na iya sanya zoben azurfa ko dukkan zoben da akayi da wani mada’dini mai daraja, musulunci bai hana ba, hasilima ado ne da kwalliya wanda musulunci kullum yake kwadaitar da musulmi akai. Amma musulunci ya haramta sanya zoben zinare ga maza kawai.
Maza na iya sanya zobe a hannun dama ko hannun hagu akaramin yatsa ko mabi da shi. Sanya zobe a hannun dama kuma a karamin yatsa ga maza yafi daraja. Hadisi ya tabbata cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Salama yana sanya zoben sa ne akaramin yatsa a hannun dama ko a hannu hagu. Makaruhi ne sanya zobe ga naminji a dogon yatsa ko manuni. Mace
za ta iya sanya zobenta duk yanda taga ya dace da kwalliyarta, hannun dama ko hagu kuma a duk yatsar da taso, amma anso hakan ya kasance bisa dabi’a da al’ada.
Babu laifi sanya zobe mai zane ko rubuto, matukar dai zanen ko rubutun bai zamo wata alamace ta mutanen banza ba ko mabiya wata mummunar akida ko addini kamar alamar gicciya na kiristoci, wato kurus (cross).
Duk wanda ya sanya zobe, to, ya motsashi kuma ya juyashi yayin alwala, ko wankan ibada ko taimama, don atabbatar da shigan ruwa karkashin sa.
Wajibi ne chire duk zoben da ruwa ba ya shiga karkashin sa. Dole ne achire zoben da aka rubuta sunan Allah a jiki lokacin shiga bayi ko lokacin zagawa don biyan bukata.
Dayawa daga cikin malamai sunyi hani daga sanya zoben soyayya ko zoben aure, hanin ya hada maza da mata baki daya. Yin hakan bidi’a ce da ta shigo cikin musulmi daga addin Nasara. Don haka musulmin kwairai ya nisanci haka.
Allah ka tsaremana Imaninmu da Mutuncinmu. Amin