’Yan Najeriya 1,317 aka kwaso daga Libya a cikin Nuwamba-NEMA

0

Hukumar Bada Agaji da Kula da ’Yan Gudun Hijira, NEMA, ta bayyana cewa ya zuwa yau an kwaso ’yan Nijeriya 1,317 daga Libya, a cikin kwanaki 10.

Babban Daraktan NEMA, Mustapha Maihaja shi ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke karbar wasu ’yan Nijeriya 116 da aka kwaso zuwa Nijeriya a yau Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa wdanda aka kwaso din na baya-bayan nan, sun iso ne a filin jirgin Murtala Mohammed da ke Lagos, a jirgin Buraq Airlines da asubahin yau.

Dama kuma kimanin ’yan Najeriya 3000 ne suka dawo don kankin kan su, a cikin watannin nan.

Maihaja wanda Kodinatan Hukumar na Shiyyar Kudu-maso-yamma, mai suna Suleiman Yakubu ya wakilta, ya kara da cewa wadanda suka dawo don kan su a cikin Nuwamba sun haura 1,295.

Share.

game da Author