Dakarun Najeriya sun yi artabu da Boko Haram a Kauyen Mainok, an rasa rayuka

0

Dakarun Najeriya da ke aiki a kauyen Mainok dake karamar hukumar Mobar a jihar Borno sun yi arangama da wasu ‘yan Boko Haram a daren Laraba inda mutane da dama suka rasa rayukan su.

Kakakin dakarun Onyema Nwachukwu ya sanar wa PREMIUM TIMES ta sakon wayan tarho cewa sun shawo kan matsalar amma ba shi da masaniyyar adadin yawan rayuka da dukiyoyin da aka rasa a batakashin.

” Sanadiyyar harin da ‘yan Boko Haram din suka kawo mana mun sami nasaran kashe wasu daga cikin su sannan suma sun kashe wasu daga cikin mu amma bazan iya fadin yawan rayuka da dukiyoyin da muka rasa ba.”

Bayan haka wani mazaunin kauyen ya fada wa PREMIUM TIMES cewa kafin ayi wannan arangama a daren Laraba ‘yan Boko Haram din sun zo sun fada musu cewa za su kai wa sojojin hari amma kada kowannen su ya tsorata ko kuma ya gudu.

” Amma tunda ba kai ka hura wa kan ka rai ba dole muka nemi mafaka a dazukan da ke zagaye da mu, da wani labarin yanzu kuke ji ba wannan.”

Share.

game da Author