Gwamnonin kasar nan sun amince gwamnatin tarayya ta kamfato dala biliyan daya daga cikin asusun rarar mai don amfani da shi wajen ci gaba da yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabacin Najeriya.
Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ne ya bayyana haka wa manema labarai bayan zaman da gwamnonin suka yi da kwamitin zantaswa da aka yi a fadar shugaban kasa a Abuja.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci wannan zaman da suka yi.
Da yake tsokaci a kai gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo ya ce adadin kudin dake cikin wannan asusun ya kai dala 2.317 wanda bisa ga haka ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz ya sanar da amincewar gwamnoni kan a ciro wadannan kudade domin yaki da Boko Haram.