Babbar kotun sauraron kara dake Maiduguri jihar Borno ta yanke wa Yahaya Umar hukuncin zama a kurkuku har na tsawon shekaru 14 tare da aiki mai tsanani dalilin kama shi da laifin aikata fyade ga wata ‘yar gudun hijira mai shekaru 13.
Iyayen Hajja sun kawo shaidun mutane 5 sannan da takardun da suke nuna cewa lalle Umaru ya aikata wannan laifi ga ‘yar su.
Iyayen Hajja sun ce Umaru ya aikata wannan mummunar aiki ne ranar 21 ga watan Satumbar 2016 bayan daukanta da ya yi ya kai ta gidan saukan baki mai suna ‘Rainbow Hotel’.
Shi kuwa Umar duk da cewa bai kawo shaida ko daya ba yayin da ake sauraron karan a kotun, ya musanta wannan zargin da aka yi masa. Ya ce tabas ya dauki Hajja amma bai kai ta gidan saukan bakin da suke fadi ba.
” Na iske Hajja na gararamba a titi, tana neman inda za ta kwana ni kuma na taimaka mata na bata wurin kwana a gida na.”
” Da garin Allah ya waye Hajja ta kama gabanta.”
Alkalin kotun Alkali Gana ya ce kotu ta gamsu da shaidun da iyayen Hajja suka mika a gaban ta saboda haka ta yanke wa Umaru zama a gidan wakafi na tsawon shekaru 14 da aiki mai tsanani sannnan yayi kira ga Iyaye da su mai da hankali ga ‘ya’yan su da sanin walwalan su.